Gwamnatin jihar kaduna karkashin gwamnan mallam nasir elrufa I ta ce ta kashe kudi naira dubu 400 ga duk mutum guda da ya kamu da cutar corona a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron kwamitin shugabanni gargajiya na arewa wand aka yi a ranar litinin a kaduna.

Gwamna el rufa I y ace idan kuwa aka yi la akari da kayan kariya da likitoci ke sakawa, kudin da aka kasha sun zarce naira dubu 400 a duk mutum guda.

Gwamnan ya alakanta karuwar cutar corona da cire takunkumin zaman gida wanda y ace hakan ne ya sa cutar ta kara yaduwa a jihar.

Gwamnan y ace yaki da corona babban al amari ne kuma aikine da ake kasha makudan kudade.

Leave a Reply

%d bloggers like this: