Rundunar ƴan sandan jihar rivers ta kama wani babban dan ta adda da ya addabi jihar da garkuwa da mutane.

Kwamishinan yan sandan jihar Joseph Mukan ne ya gabatar da dan ta addan a helkwatar rundunar bayan sun kamashi a yau asabar.
An kama honest digbara wanda aka fi sani da boboski bayan jami an yan sanda sun samu bayanan sirri a kansa.

Koda a kwanakin baya sai da gwamnan jihar wike Nyesom ya sanya ladan naira miliyan 30 ga duk wanda ya kawoshi.

Kwamishinan yan sandan jihar ya bayyana cewar manyan ayyukan ta addanci da ke faruwa a jihar akwai sa hannun dan ta addan wanda a yanzu yake hannunsu.
Ya kara da cewa sun samu nasarar kamashi ne hadin gwiwa da jami an tsaron sa kai a yankin karamar hukumar tai na jihar rivers