Mujallar Matashiya ta saka rana da lokacin da za a gudanar da horo ga matasa masu sha’awar koyon aikin jarida da ɗaukar hoto.

Za a yi horon ne a ofishin mujallar Matashiya da ke lamba 1B france road a Kano.

Sai dai an gindaya ƙa’idoji ga masu son koyon aikin jarida har sai sun kawo shaidar karatun na guda cikin jerin waɗannan

Hausa

English

Arabic

Mass Comm

History

Kuma ana buƙatar waɗanda za su koyi aikin jarida su zo da takardun shaidar karatun ɗaya daga ciki.

Za a bayar da horon aikin jarida har tsawon mako uku yayinda masu ɗaukar hoto za su yi mako biyu.

An tura rana da lokacin ta hanyar Gmail ɗin waɗanda suka aiko da buƙatar hakan kamar yadda aka nema a baya.

2 thoughts on “An saka rana da lokacin horas da aikin jarida/ɗaukar hoto kyauta – Mujallar Matashiya”

Leave a Reply

%d bloggers like this: