Gwamnatin jihar kaduna ta bayyana cewar  za ta kara kudin haraji a tashoshin hawa da saukar motoci na jihar.

Haka kuma gwamnatin za ta rufe haramtattun tashoshin mota don bunkkasa hanyar kudin jiga a jihar.

Shugaban hukumar tattara haraji a jihar Dakta Zaid Abubakar ne ya shaida hakan yana mai cewar, tashin haramtattun tashoshin zai fara aiki ne daga sati mai  zuwa.

Zaid Abubakar ya kara da cewar, za a yi hakan ne don bunkata hanyoyin shigar kudi na jihar tare da tsare rayuka da lafiyar al umma, don ganin an tabbatar da tsaro a fadin jihar.

Sannan ya bukaci direbobin motar da su yi biyayya ga wannan hukunci na gwamnati don ganin an cimma nasarar abinda ta saka a gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: