Wasu yan bindiga sun sace wasu alaƙalan kotun sharia r musulunci a Zamfara.

An sace alkalan ne a kan hanyarsu ta dawowa daga tafiya bayan sun je karo karatu.
An yi garkuwa da Mallam Shafi u Ibrahim Jangebe da malam Sabiu Abdullahi a yayin da suke kan hanyar komawa gida a tsakanin kananan hukumomin zurmi da jibiya.

Rahotanni sun nuna cewar alƙalan sun je karo karatu ne a wata makaranta al nahda international da ke jamhuriyar nijar.

Mallam Hassan guda ne cikin yan uwan daya daga cikin alkalan da aka sace yace, masu garkuwa da mutanen sun kirashi a waya tare da neman kudin fansa naira miliyan 10 duk mutum guda.
Sai dai har yanzu ba a cimma matsaya akan kudin da za a biya ba.
Mai Magana da yawun rundunar yan sandan jihar zamfara SP Muhammad Shehu ya ce yana da masaniya a kan lamarin, sai dai har yanzu ba su samu rahoto a kan inda lamarin ya faru ba.
Tsawon mako guda kenan da aka sace alkalan biyu a kan haryarsu ta dawowa daga tafiya