Connect with us

Labarai

Ƴan sanda sun kama masu garkuwa da mutane guda 18 tare da ƴan fashi 8

Published

on

Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta yi holen masu aikata laifuka dabab daban  har mutane 36 a jihar.

Kwamishinan yan sandn jihar Olugbenga Adeyanju ne ya gabatar da masu laifin ga yan jaridu a harabar helkwatar rundunar.

Cikin mutanen  da aka kama akwai mutane goma sha takwas 18 da ake zargi da aikata laifin garkuwa da mutane, sai mutane 8 da ake zarginsu da aikata fashi da makami sannan mutane bakwai da ake zargi da aikata fyade sai mutum uku da ake zarginsu da satar motoci.

Rundunar ta yi nasarar kwato bindiga kirar AK47 guda uku tare da alburusai masu yawa, haka kuma ta kubutar da ababen hawa na mutanen da aka sace.

Bayan rundunar ta yi holen masu laifin sannan ta karrama wasu mutane da suke bawa rundunar gudunmawa wajen ganin an samar da tsaro a fadin jihar.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Mutane Uku Sun Rasa Rayukansu A Harin Da Yan Bindiga Suka Kai Filato

Published

on

Akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu ciki har da wani dalibin jami’a a lokacin da ‘yan bindiga suka kai musu hari a ranar Alhamis a jihar Filato.

Maharan sun hallaka mutanen ne a lokacin da suka kai musu hari a kauyen Butura da ke cikin karamar hukumar Bokkos ta Jihar da misalin karfe 9:00, inda zuwan su ke da wuya suka bude wuta akan mutanen kauyen.

Rahotanni sun bayyana cewa dalibin da harin ya rutsa dashi ya na aji na biyu ne a jami’a, inda ya ke karantar fannin kimiyyar na’ura mai kwakwalwa.

Wasu majiyoyi daga kauyen sun bayyana cewa bayan hallaka dalibin hakan ya sanya daliban jami’ar suka gudanar da zanga-zangar.

Jihar Filato dai na daya daga cikin Jihohin Najriya da ke fama da yawaitar hare-haren ‘yan ta’addan a yankunan Jihohin Kasar.

 

 

 

 

Continue Reading

Labarai

Kungiyoyin Fararen Hula 45 Sun Nemi EFCC Ta Fara Binciken Sanata Rabi’u Kwankwaso

Published

on

Gamayyar wasu Kungiyoyin fararen hula 45 a kano sun aikewa da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa EFCC wata takarda akan ta fara gudanar da bincike akan tsohon gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kungiyoyin karkashin kungiyar fafutukar tabbatar da adalci ga kowa sun bukaci hukumar da ta fara gudanar da bincike akan Kwankwaso dangane da yadda ya jagoranci mulkin kano a baya.

Wasikar mai dauke da sa hannun shugabannin kungiyar Auwalu Ibrahim da Dave Ogbole a madadin sauran kungiyoyi sun yi kira ga EFCC da ta bude sabon shafin bincikar sanata Kwankwaso.

Gamayyar kungiyoyin sun bayyana cewa binciken ya zama wajibi domin ganin an bi sahun dukiyar Jihar, duba da yadda mutane ke cikin halin kunci a Jihar.

Kazalika kungiyoyin sun ce bincikar Kwankwaso zai cike dukkan wani gibi da ke akwai na tabbatar da yaki da cin hanci da rashawa a gwamnatocin da suka shude.

Kungiyoyin sun bukaci hukumar ta EFCC da ta yi duk mai yuwuwa wajen ganin gwamnatin Kwankwaso ta yi bayanin akan yadda aka sarrafa dukiyar Jihar a lokacin ya na mulkar Jihar.

 

 

 

 

Continue Reading

Labarai

Immigration Za Ta Sanya Ido Akan Shige Da Fice Na Tsohon Gwamnan Kogi

Published

on

Hukumar shige da fice ta Kasa wato Immagration ta bayyana cewa tsohon gwamnan Jihar Kogi Yahya Bello na daya daga cikin wadanda za ta sanya idanu akan shige da ficensu.

A wata takardar da mataimakin shugaban hukumar ya sanyawa hannu ya umarci dukkan jami’an hukumar da su kama Yahaya Bello a duk lokacin da ya yi yunkurin ficewa daga Kasar.

Sanarwar ta bayyanawa jami’an cewa a dukkan wata iyaka ta kasar da suka ga tsohon gwamnan na Kogi su kamashi.

Umarnin hukumar na zuwa ne a dai-dai lokacin da rundunar ‘yan sanda ta kasa ta janye jami’anta daga gidan tsohon gwamnan.

Hukumar ta bai’wa jami’annata umarnin ne bisa yadda hukumomi a kasar suke nema Yahya Bello ruwa a jallo bisa zarginsa da badakalar wasu kudade a lokacin da ya na kan kujerar gwamnan Jihar.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: