Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El’rufa’I ya sanya hannu akan dokar fidiye masu aikata laifin fyade a jihar.

Dokar dai za ta bada damar yanke hukunci mai tsauri kamar kisa ko kuma dandaƙa

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya rawaito cewa  kunshin  bayanin fidiye masu aikata laifin dokar  ta tanadi hukuncin  kisa ga duk wanda aka samu yayiwa yan kasa da shekara 14 fyade.

Ka zalika dokar tayi bayanin za’a’iya hadawa mutum hukunci 2 lokaci guda baya ga fidiye mutum sannan a daure shi har na tsawon rayuwarsa.

Matsalar fyade ta addabi Najeriya musamman a wannan shekarar ta 2020 koda a watanni baya saida aka samu gawar wata yarinya da aka yar da ita cikin wani masallaci bayan anyi  mata fyade.

Leave a Reply

%d bloggers like this: