Gwamnatin tarayyar najeriya ta gano wasu matafiya da ke zuwa ƙasar daga ƙashen ƙetare na gabatar da shaidar gwajin cutar corona ta jabu.

Kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa a kan yaki da cutar corona karkashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, sune suka gabatarwa da fadar shugaban kasa jawabin hakan a yayin wani taro da aka gudanar a Abuja.

Kwamitin y ace mutanen da suke zuwa suna nuna shaidar gwajin corona ta jabu wanda hakan ke barazana ga al ummar kasar.

Kwamitin ya bayyana cewar kafin bada damar saukar jirage daga kasashen ketare, sai da aka cimma matsaya a kan za a gwada duk wani mutum da zai zo najeriya  awanni 74 kafin tasowarsu daka kowacce kasa.

Sai dai kasashe 13 da aka bawa damar shigowa najeriya sun karya ka idar, bayan da aka samu wani jirgi dauke da masu shaidar gwajin cutar ta jabu.

Kwamitin ya bukaci kasashen da su sanya ido tare da tabbatar da cewar an gwada duk wani mutum kafin tahowa daga kasar da yake.

Leave a Reply

%d bloggers like this: