Hukumar Hizbah a jihar Kano ta sha alwashin cigaba da kakkaɓe ayyukan ɓata gari a faɗin jihar.

Kwamandan hukumar Ustaz Haroon Ibn Sina ne ya tabbatar da hakan yayin da ya ziyarci kasuwar kayan gwari da ke kwanar gafan a ƙaramar hukumar garun mallam a kano.
Mallam Ibn Sina ya tabbatar da cewar hukumar a shirye take don ganin an tsaftace kasuwar ta hanyar cimma yarjejeniya da mahukuntan kasuwar don ganin an kai dakarun hukumar lungu da saƙo na kasuwar saboda su sa ido a kan masu hada hada a ciki.

Ya ƙara da cewar ya zama wajibi a kawar da ɗakunan wucin gadi na kasuwar don toshe mafaka ga ɓata gari.

Kasuwar dai ta yi suna wajen samun mutanen da ke aikata baɗala wanda hakan ya sa hukumar ta kai ziyarar bazata.