Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana damuwa kan matakan da kasashen Turai ke dauka na yakar annobar COVID-19, na rage yawan kwanakin killace bakin da ke zirga-zirga a tsakaninsu.

Hukumar ta WHO ta kuma koka kan hadurran da ma’aikatan lafiya ke fuskanta a sassan duniya yayin yakar annobar.

Yayin wata ganawa da manema labarai a baya bayan nan, babban daraktan hukumar lafiyar ta duniya a Turai Hans Kluge,

yace matakan wasu kasashen nahiyar na rage tsawon kwanakin killace mutanen da suka kamu da cutar coronavirus, na tattare hadarin gaske, la’akari da cewar yanzu haka yawan mutanen dake kamuwa da cutar na sake hauhawa bayan saukin da aka samu.

Wasu daga cikin kasasshen da suka rage kwanakin killace marasa lafiyar kuwa sun hada da Birtaniya da Ireland da suka mayar da kwanakin daga 14 zuwa 10, yanzu haka kuma kasashen turai da dama cikinsu harda Croatia da Portugal na nazarin daukar irin wannan mataki, wanda tuni Faransa ta zartas duk da cewa a baya bayan nan sama da mutane dubu 10 suka kamu da cutar ta corona cikin kasar a rana daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: