Gwamnatin jihar Kaduna ta bada hutun kwanaki uku don ta aziyya da alhinin rasuwar mai martaba sarkin zazzau Alhaji Shehu Idris.

Mashawarci na musamman a kan kafafen yada labarai da sadarwa na gwamann kaduna Muyiwa Adekeye ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce za a bude ma aikatun gwamnati a ranar litinin da talata amma ba za a gudanar da aiki kamar yadda aka saba ba, a ranar laraba kuwa za ta zamto ranar hutu don alhinin rasuwar sarkin zazzau.

Sarkin zazzau Marigayi Alhaji Shehu Idris ya rasu a jiya lahadi a wani asibitin sojoji da ke kaduna kuma an binneshi a makabartar binne sarakuna da ke zariya bayan an sallaceshi a jiya lahadi da misalin karfe 5 35  na yamma.

Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya, an nadashi a matsayin sarki a ranar 15 ga watan fabrairu na shekarar 1975, ya mulki masarautar zazzau tsawon shekaru 45.

Dubban mutane ne suka halarci jana izar sarkin a birnin zazzu.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: