Corona VirusCorona Virus

Cutar corona na cigaba da raguwa a Najeriya bayan da aka samu sabbin mutane 97 masu dauke da ita, yayinda mutane 138 suka warke a fadin kasar jiya lahadi.

A wannan lokutan dai ana samun  raguwar wadanda cutar ke harba a ƙasar, sannan ana samun adadi mai yawa na mutanen da ake sallama daga wuraren killace masu ɗauke da cutar a sassa daban-daban na ƙasar.

A yanzu haka dai mutane 57,242 ne ke ɗauke da cutar yayinda mutane 48,569 suka warke, sannan aka samu mutane 1,098 waɗanda cutar ta hallaka.

Cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a najeriya NCDC ce ta wallafa adadin mutanen a daren jiya lahadi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: