Gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje ya mika sakon ta aziyyarsa a bisa rashin mai martaba sarkin zazzau Alhaji Shehu Idris.

Cikin sanarwar da babban sakataren yada labaran gwamnan kano Mallam Abba Anwar ya fitar, gwamna Ganduje ya bayyana marigayi sarkin zazzau a matsayin shugaba abin koyi kuma jigo a najeriya, wanda ya bayyana rashinsa a matsayin babban rashi bisa ga dattako tare da jajircewa wajen tabbatar da girmama al umma.

Gwamna Ganduje ya miƙa saƙon ta aziyya ga iyalan marigayi sarki, da masarautar zazzzau da al ummar zariya da ma al ummar najeriya baki daya a bisa babban rashi da aka yi.

Sannan yayi addu ar Allah ya jikansa ya gafarta mawa mai martaba sarki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: