Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta tabbatar da nasarar Godwin Obaseki  na jam iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Edo a Najeriya.

Obaseki ya doke babban abokin karawarsa na jam iyyar APC fasto osagie iye-iyamu da kuri u 307,955 yayin da abokin takararsa na jam iyyar apc iye iyamu ya samu kuri u 223,619.

Wannann  ne karo na biyu da obaseki yake doke abokin karawarsa iye iyamu, kamar yadda a shekarar 2016 ya samu nasara a kansa lokacin iye iyamu yana jam iyyar pdp obaseki kuwa yana jam iyyar apc.

An gudanar da zaben ne a ranar asabar 19 ga watan da muke ciki, yayin da aka sanar da sakamakon zaben a jiya lahadi.

Ko da shugaban kasa Muhammadu Buhari sai da ya taya Gwamna obaseki murnan nasarar da yayi a zaben.

Gamnan Obaseki dai shine gwamna  mai ci a jihar edo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: