Wasu da ake zargin ƴan fashi ne sun yiwa wata fyaɗe sannan suka harbi wata a wata coci da ke Abakaliki na jihar Ebonyi.

Ƴan fashin sun shiga cikin cocin a yayin da wasu maza da mata suke gudanar da wasan kwaikwayon gwaji da misali ƙarfe ɗaya na daren laraba.

Wasu daga cikin matasan da suke wasan kwaikwayon na gwaji sun tsere a yayin da maharan suka shiga cikin cocin

Wani daga cikin masu alaƙa da cocin ya tabbatar da cewar, maharan sun yi awon gaba da wasu kayayyaki mallakin cocin.

Harin ya faru ne daren jiya wayewar garin yau laraba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: