Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta gudanar da wani zaman sulhu tsakaninta da ƙungiyar kwadago ta ƙasar.

Sanarwa hakan ta fito daga mataimakin daraktan gudanarwa na hulɗa da jama’a na ƙungiyar.
Gwamnatin ta saka gobe alhamis 24 ga watan satumban da muke ciki don tattaunawa tare da samar da matsaya kan ƙarin farashin man fetur da wutar lantarki wanda ta yi a baya.

Za a gudanar da zaman ne a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Kafin hakan, ƙungiyar ta yi barazana shiga yajin aikin gama gari a bisa ƙarin farashin wutar lantarki da man fetur, wanda gwamnatin Najeriya ta yi a watan da muke ciki.
Haka ne ya sa ƙungiyar ta shirya zanga zanga tare da yajin aiki a fadin ƙasar