Mahukunta a ƙasar saudiyya sun saka wasu sharuɗa kafin bada damar gudanar da ibadar umarah a ƙasar.
Hukumomin sun ce kashi 30 cikin 100 za a bari su yi ibadar umarah a cikin masallacin harami a kullum.
Yayin da kashi 75 za su kasance suna gudanar da ibadar a bayan harabar masallacin.
Sai kuma kashi 75 za su ke zuwa masallacin madina, wannan tsarin masana lafiya suka bayar don ganin an daƙile yaɗuwar cutar corona a ƙasar.
Haka kuma tsarin zai fara aiki ne daga ranar huɗu ga watan Oktoban da za mu shiga, sai dai mahukuntan ƙasar sun bayyana cewar, za su bayyana matakan da za a bi ga mutanen da suke ƙashen ƙetaren saudiyya daga ranar ɗaya ga watan Nuwamba na shekarar da muke ciki.
An dakatar da gudanar da ibadar Umarah ne saboda ɓullar cutar Corona wadda a baya ake samun adadi mai yawa na mutanen da suke kamuwa da ita a ƙasar