Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce akwai yuwuwar cutar Korona ta hallaka mutane kusan miliyan uku a faɗin duniya.

Daraktan agajin gaggawa na hukumar Micheael Pyan ya ce, matuƙar ƙasashen duniya ba su haɗa kai wajen daƙile cutar ba akwai yuwuwar a ƙara samun mutane miliyan ɗaya da cutar za ta hallaka a nan gaba.
Hukumar ta ja hankalin mutane da su bi dukkan matakan kariya daga cutar kamar, wanke hannu da ruwa mai gudana,kaucewa taɓa fuska da hannun da ba a wanke ba, bayar da tazara, da kuma rufe baki da hanci da safa.

Cutar Korona dai ta hallaka kusan miliyan ɗaya a yanzu cikin ƙasashe daban daban na faɗin duniya.
