Sarkin Shinkafi mai martaba Alhaji Muhammad Shuwari Isa ya naɗa Ambasada Yunusa Yusuf Hamza a matsayin falaƙin shinkafi.

Masarautar shinkafi ta bayyana cewar an zaɓi Ambasada Yunusa ne ganin yadda yake fafutuka don kawo cigaba ga matasa a Najeriya.
Ambasada Yunusa Hamza Jarman matasan arewa, ya ja hankalin matasa da su kasance masu amfani da ilimin da suke da shi wajen tabbatar cigaba a rayuwarsu.

Yayin da yake jawabin godiya jim kaɗan bayan bashi shaidar zama falaƙin shinkafi, Ambasada Yunusa ya nuna godiyarsa ga masarautar a bisa yadda aka zaɓoshi tare da bashi wannan dama don hidimtawa al umma.

An bashi shaidar zama Falaki a jiya Asabar a masarautar shinkafi, a garin shinkafi da ke jihar Zamfara.