Wasu a ƙungiyar kare hakkin dan adam na majalisar dinkin duniya sun bukaci a saki matashin da yayi batanci ga annabi S.A.W.

Cikin wata sanarwa da kwararru guda 10 kan kare hakkin dan adam suka fitar, sun nemi a soke hukuncin kisa ta hanyar rataya da aka yankewa matashin Yahaya Sharif Aminu mai shekaru 22 a duniya.
A cewarsu, yin waka ba laifi bane, kuma hakan ya sa suke rokon a yafewa matashin.

Wata kotun sharia r muslunci ce dai ta yankewa yahaya sharif hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ta sameshi da laifin yin batanci ga shugaba fiyayyen halitta annabi Muhammad S.A.W.
