A sakamakon janye ƙarin farashin ƙungiyar kwadago ta janye yajin aikin da ta shirya tsunduma a yau.

Gwamnatin tarayya ta janye ƙarin kuɗin wutar lantarki a daidai lokacin da ƙungiyar kwadago ta shirya tsunduma yajin aiki.

Ƙaramin ministan kwadago a Najeriya Festus Keyamo ne ya sanar da hakan a shafinsa na tiwita.

Wannan ne dalilin da ya sa ƙungiyar kwadago a Najeriya NLC ta janye tsunduma yajin aikin da ta shiya shiga a yau Litinin.

Sai dai janyewar ƙarin farashin wutar iya na makonni biyu ne kacal, kafin gwamnatin ta yi duba a bisa matakin da za ta ɗauka na gaba.

Ƙungiyar kwadago ta shirya shiga yajin aikin ne sakamakon ƙarin farashin wutar lantarki da man fetur wanda ta yi makonni biyu da suka wuce.

Leave a Reply

%d bloggers like this: