Wani direban mota ya rasa ransa a sanadiyyar wani hatsarin mota da ya faru a kan titin Abuja zuwa lokoja.
Direban motar kirar Sharon, motar ta kwace a hannunsa ne a yayin da yake tuƙi a daidai lokacin da wata mota kirar daf ta tinkaro gabansa.
Wani da alamarin ya faru a kan idonsa ya shaida cewar, baya ga direban motar Sharon da ya rasu akwai wani da aka kaishi asibiti bayan ya samu mummunan rauni.
Lamarin ya faru a safiyar asabar lokacin ana tsaka da ruwan sama kamar yadda wani da alamarin ya rafu a kan idonsa ya bayyana.
Kwamandan hukumar kiyaye afkuwar haddura ta kasa frsc na shiyyar ACC Abubakar Shehu ya bayyana cewar, sun mika gawar direban zuwa babban asibitin Abaji tare da wanda yaji raunin.
Shi kuwa direban babbar motar sun miƙashi ga rundunar yan sanda mafi kusa, sai dai ya alaƙanta afkuwar hatsarin da gudun wuce sa a wanda yayi sanadiyyar direban ya kasa sarrafa motar.


