Akalla mutane 40 suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan sama a jihar jigawa.

Hukumar bada agajin gaggawa a jihar SEMA ita ta bayyana hakan kamar yadda babban sakataren hukumar Alhaji Sani Babura ya bayyana.
Ya ce hukumar ta shirya tsaf don ganin ta kai tallafi ga wadanda ruwan ya yiwa ta adi.

Ya kara da cewa dubban mutane ne suka rasa muhallinsu, wasu kuwa sun rasa gonakinsu a sanadin ruwan sama na bana.

Wannan ne ya sa gwamnatin jihar ke bukatar tallafi daga gwamnatin tarayya don ganin an ragewa mutanen radadin abinda ya samesu.
Ruwan saman bana yayi ambaliya a wasu daga cikin jiohohin Najeriya ciki har da jihar Nijer, benue da Taraba