Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa daliban makarantar firamare da sakandire a jihar za su koma makaranta daga ranar 5 ga watan Oktoba mai kamawa.

Kwamishinan ilimi a jihar Dakta Lawal Charanchi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya.

Ya ce daliban firamare daga aji 1 zuwa 3 za su ke zuwa makaranta da safe, yayinda yan aji 4 zuwa 6 za su ke zuwa makaramtun da yamma.

Sauran yan karamar sakandire kuma za su ke zuwa makaranta da safe yayin da yan babban sakandire za su ke zuwa makaranta da yamma.

Charanchi ya kara da cewa gwamnatin ta yanke shawarar hakan ne don a bawa daliban daman kammala zango na biyu a karatunsu, kuma za su ke daukar darasi kafin fara jarrabawar kammala zango na biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: