Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ƙaddamar da motocin hawa na gwamnatin Kano wato Kano Line guda goma.

Yayin da yake jawabin lokacin da yake ƙaddamar da motocin, Ganduje ya yabawa shugaban kamfanin zirga zirga na Kano Line bisa yadda suke kawo cigaba wajen gudanar da zirga-zirga a cikin tsari.

Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta duƙufa wajen inganta hanyoyin zirga zorga, shi yasa ake samar da gadar ƙasa don kyautata harkar sufuri a jihar.

Gwamna Ganduje ya buƙaci al’ummar jihar Kano da su cigaba da ta’ammali da motocin sufuri na Kano Line don ciyar da jihar gaba.
Kwamishinan sufuri a jihar Kano Muhammad Mahmud Santsi da Shugaban kamfanin Kano Line Bashir Nasiru Aliko Ƙoƙi sun tabbataar da cewar, za su cigaba da kawo sauyi mai ma’ana ta yadda za a yi alfahari da sabbin tsare tsaren da za su kawowa harkar sufuri.
An ƙaddamar da motocin ne a harabar gidan gwamnatin Kano a yau Laraba.