Masu zabar sarki a masarutar zariya sun dukufa ,don sake zabo wasu sunayen mutanen da za’a mikawa gwamnan jihar don zabar sarki a ciki.
Hakan na zuwa ne bayan da gwamnan jihar kaduna Nasiru El’Rufa’I bai zabi ko mutum guda ba cikin sunan mutane biyu da masu zabar sarkin suka mikawa gwamnatin jihar.
Mai magana da yawun gwamnan muyiwa Adeyeye yace sakataren gwamnatin jihar shi ya sanar da haka, kazalika gwamantin jihar tabawa masu zabar sarkin sake zabo mutanen don nada sarki a masarautar.
A makon da ya gabata ne gwamna El’Rufa’I a shafinsa na twitter ya sanar da cewa zai nada sabon sarki a masarautar bayan ya gama karanta wani littafin tarihin masarautar da aka rubuta a shekarar 1960.