Najeriya ta cika shekaru 60 da samun ‘yan cin kai daga turawan mulkin mallakar kasar birtaniya wato lngila, a shekarar 1960 bayan shafe shekaru masu yawa suna mulkar kasar.

A wancan lokacin shuwabanin najeriya da suka hada da Sir Abubakar tafawa balewa da kuma dr Nmandi Azikuye sune a matsayi shugabanin kasa da kuma firaiminista.
Kafin daga baya sojoji suyi musu juyin mulki tare da kashe tafawa balewa karkashin jagorancin Janar Igwan Ironsi lokaci jihar lagos itace babban birin tarayyar Najeriya.

Izuwa yanzu shuwagabanni 13 suka mulki najeriya, ko wane irin cigaba najeriya ta samu daga wancan lokacin zuwa yanzu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya godewa yan Najeriya bisa bashi goyon baya da sukeyi akan yadda yake gudanar da mulki a ƙasar.
Shugaban ya fadi haka ne lokaci da yakewa al’ummar kasa jawabi , dangane da cikar Najeriya shekaru 60 da samun yancin kai daga hannu turawan kasar burtaniya.
Sannan shugaban ya yabawa tsoffin shuwagabannin kasar da suka jajirce har najeriya ta samu yancin kanta a wancan lokacin.
Ka zalika shugaban yayi tsokaci musamman akan tabarbarewar tsaro, yayin da yace ana shigar siyasa ne cikin lamarin shi yasa matsalar taki karewa.
haka kuma ya jaddada cewa yana kokari don samar da shugabanci nagari tare dayin amfani da duk wasu ma’adanai da kasar take dasu domin amfin yan kasa.
Da yake bayani akan Karin farashin man fetur shugaban ya bayar da misali da kasashen chadi ,ghana,da kuma kasar misira inda yace dukkannin kasashen suna sayar da man sama da 300 kan wacce lita, don haka hankali ba zai dauka ba ace najeriya tana sayar da shi a farashinsa Kamar na baya.
Daga karshe kuma ya bayyana cewa yana fata shekara ta 2021 a samu cigaban da ake fatan samu a najeriya baki daya