Connect with us

Labarai

Shekaru 60 da samun yancin kai a Najeriya, abubuwan da ya kamata ku sani

Published

on

Najeriya ta cika shekaru 60 da samun ‘yan cin kai daga turawan mulkin mallakar kasar birtaniya wato lngila, a shekarar 1960 bayan shafe shekaru masu yawa suna  mulkar kasar.

A wancan lokacin shuwabanin najeriya da suka hada da Sir Abubakar tafawa balewa  da kuma  dr Nmandi Azikuye  sune a matsayi shugabanin kasa da kuma firaiminista.

Kafin daga baya sojoji suyi musu juyin mulki tare da kashe tafawa balewa karkashin jagorancin Janar Igwan Ironsi lokaci  jihar lagos itace babban birin tarayyar  Najeriya.

Izuwa yanzu shuwagabanni 13 suka mulki najeriya, ko wane irin cigaba najeriya ta samu daga wancan lokacin zuwa yanzu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya godewa yan Najeriya bisa bashi goyon baya da sukeyi akan yadda yake gudanar da mulki a ƙasar.

Shugaban ya fadi haka ne lokaci da yakewa al’ummar kasa jawabi , dangane da cikar Najeriya shekaru 60 da samun yancin kai daga hannu turawan kasar burtaniya.

Sannan shugaban ya yabawa tsoffin shuwagabannin kasar  da suka jajirce  har najeriya ta samu yancin kanta a wancan lokacin.

Ka zalika shugaban yayi tsokaci musamman akan tabarbarewar tsaro, yayin da yace ana shigar siyasa ne cikin lamarin shi yasa matsalar taki karewa.

haka kuma ya jaddada cewa yana kokari don samar da shugabanci nagari tare dayin amfani da duk wasu ma’adanai da kasar take dasu domin amfin yan kasa.

Da yake bayani akan  Karin farashin man fetur shugaban  ya bayar da misali da kasashen chadi ,ghana,da kuma kasar misira inda yace dukkannin kasashen suna sayar da man sama da 300 kan wacce lita, don haka hankali ba zai dauka ba ace najeriya tana sayar da shi a farashinsa Kamar na baya.

Daga karshe kuma ya bayyana cewa yana fata shekara ta 2021 a samu cigaban da ake fatan samu a najeriya baki daya

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Tsadar Karatu Na Iya Sa Rabin Ɗaliban Jami’a Su Gudu – ASUU

Published

on

Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ta ce kashi 50% na ɗaliban da ke karatu na iya ajiyewa saboda tsadar karatu da ake ciki a ƙasar.

Shugaban ƙungiyar Frafesa Emmanuel Osodoke ne ya bayyana haka ya ce nan da shekaru biyu zuwa uku masu zuwa ɗaliban da ke karatu a jami’o’in ƙasar kashi 50% daga ciki na iya ajiye karatun nasu.

A wata hira da aka yi da shugaban a gidan talabiji na Channels ranar Lahadi da daddare, ya gargaɗi ɓangaren ilimi na ƙasar da su farga a kan abinda ka iya faruwa.

Sai dai ya alaƙanta ƙara kuɗin da jami’o’i su ka yi da mafi ƙarancin albashin da ake biya na naira 30,000 a ƙasar.

Sannan ya ce akwai hatsari mai yawan gaske idan aka samu ƙarin matasa masu yawa da su ka bar makaranta.

Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata gwamnatin Najeriya ta ce ta ƙarawa malaman jami’a albashi da kashi 30 ga masu matsayin farfesa.

Continue Reading

Labarai

Gobara Ta Kama A Kotun Ƙoli Ta Najeriya A Abuja

Published

on

Rahotanni daga baban birnin tarayyar Najeriya Abuja na tabbatar da cewar kotun ƙoli ta kama da wuta.

Ofishin alƙalai uku aka ruwaito sun ƙone bayan tashin gobarar.

Godan jaridar Arise ya ruwaito cewar, wutar ta kama wai ɓangare na cikin kotun.

Sai dai ba a san sanadin tashin gobarar ba.

Wannan dai itace gobara da aka yi a kusa-kusa wadda ta shafi ofishin gwamnati.

Ko a watan Mayun shekarar da mu ke ciki, gobara ta kama a rundunar sojin samar Najeriya.

Yayin da a shekarar da ta gabata ta 2023 ma’aikatar kuɗi ta tarayya wani ɓangare ya kama da wuta.

Continue Reading

Labarai

Amuruka Ta Gargaɗi Ƴan Ƙasar Mazauna Najeriya Kan Ziyartar Wasu Jihohi Har Da Kano

Published

on

Ƙasar Amurka ta gargaɗi ƴan ƙasar mazauna Najeriya da su kiyaye wajen ziyartar wasu jihohi da ka iya faɗawa cikin hatsari.

Sanarwar na zuwa ne bayan gudanar da wani bincike da su ka gano an samu ƙaruwar aikata manyan laifuka a jihohin.

Jihohin sun haɗa da Borno, Adamawa, Yobe, Kogi, Bauchi, Kaduna, Kano, Gombe, Bayelsa, Rivers, Enugu da jihar Bayelsa.

Sauran jihohin su ne Imo, SokOto, Zamfara, Katsina, da jihar Abia.

Ƙasar ta gargaɗi mutanenta da su kiyaye wajen ziyartar waɗannan jihohi domin su na iya faɗawa cikin tarkon masu garkuwa da mutane ko wasu miyagun laifuka.

Binciken da su ka yi sun gano cewar masu satar mutane domin neman kuɗin fansa na amfani da ƙarin mutane a wasu sassa domin cimma muradinsu.

Sannan gwamnatin Amurukan ta buƙaci ƴan ƙasar mazauna Najeriya da su ƙara sanya idanu a kan dukkanin zirga-zirgarsu don gudun faɗawa hatsari.

 

 

 

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: