A Najeriya an koma makarantun firamare da sakadire a jihohin kwara katsina da kebbi bayan shafe watanni shida suna rufe.

An koma makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihohin uku bayan an yi feshin magani a makarantun.

Tun a makon da ya gabata mun kawo muku labarin cewar jihar katsina ta sanar da buɗe makarantun kamar yadda suka tsara lokacin ɗaukar darasi zai kasance safe da yamma don kaucewa Cunkoson ɗaliban.

ɗaliban za su sanya safar baki da hanci tare da wanke hannu hadi da bada tazara yayin da ake ɗaukar darasu da kuma bayan an fita hutun taƙaitaccen lokaci.

Ko da a jihar kano ma gwamnatin jihar ta sanar da buɗe makarantun boko da na islamiyya daga ranar 11 ga watan da muke ciki.

An rufe makarantu a Najeriya don kaucewa yaduwar cutar korona wadda ta bulla tun a watan maris ɗin da ya gabata.

Sai dai gwamnatin ta dubi yadda aka samu saukin yaduwar cutar tare da ɗaukar matakan kariya wanda hakan ya bada dama ga gwamnonin jihohi don duba yuiwar buɗe makarantu a jihohinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: