Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Siyasa

Damarka na hannunka – sabon salon siyasa a Kano

Jam iyyar APC a jihar kano yankin karamar hukumar nassarawa tsagen gidan Abba Boss sun gudanar da gangamin wayar da kai ga al umma a jiya lahadi.

An shirya taron ne don wayar da kan jama a don ganin sun jajirce sun tura wakilai da za su jagorancesu a mataki daban daban.

Muhammadu Aminu Adamu wanda aka fi sani da Abba Boss yace sun shirya gangamin sakamakon ƙaƙabe da wasu a cikin siyasar keyi na ganin sun saka wadanda za su wakilci mutane ba tare da yardar al ummar ba.

Ya ƙara jaddada aniyarsa na cewa yana nan daram cikin jam iyyar APC, kuma suna a ƙara ingantata don samun nasararta a zaɓe mai zuwa.

Ya kara da cewa sun kira gangamin da sunan (damarka na hannunka) saboda su nunawa mutane cewa suna da yanci su zabi mutumin da suke ganin zai musu adalci tare da gudanar da ayyukan da jama a suke bukata.

An gudanar da taron ne a sakatariyar jam iyyar APC ta karamar hukumar Nassarawa a jihar kano, kuma cincirondon al umma maza da mata ne suka halarci taron ciki har da manyan yan jam iyyar APC da shugaban jam iyyar na ƙaramar hukumar Nassarawa.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: