Labaran jiha
Yan bindiga sun yi awon gaba da manoma 22 a Katsina


Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun sace wasu manoma a jihar Katsina.

Aƙalla manoma 22 aka sace a gonakinsu a sabon garin Mallamawa na ƙaramar hukumar Jibia.
Kakakin yan sanda a jihar Katsina S.P Gambo Isah ya tabbatar da faruwar al amarin.

Har yanzu ana fargabar satar mutane a jihar Katsina musamman a yankin Jibia, Batsari, Fskari, Funtua da ƙanƙara.


Labaran jiha
Gwamnatin Kano Za Ta Buɗe Cibiyoyin Koyon Sana’o’in Dogaro Da Kai


Gwamantin jihar Kano ta ce za ta buɗe cibiyoyin koyon aikin sana’o’in dogaro da kai a jihar.

Sannan gwamnatin jihar Kano ta rage kashi 50 cikin ɗari na rijistar shiga manyan makarantu a jihar.
Ragin ya shafi iya ɗalibai ƴan asalin jihar Kano ne kaɗai.

A wata sanarwa da kwamishinan ilimi mai zurfi a jihar Dakta Yusuf Ibrahim Ƙofar Mata ya sanyawa hannu, sanarwar ta ce an yanke hukuncin ne yayin wata ganawa da da gwamnan ya yi da shugabannin manyan makarantu a jihar.

Sanarwar ta ce an yi haka ne domin baiwa ɗalibai a jihar damar samun ilimi.

Haka kuma gwamnatin za ta buɗe cibiyoyin koyon sana’o’in dogaro da kai a jihar yadda matasa za su tsaya da ƙafarsu.
Gwamnatin ta ce ta na mayar da hankali domin bayar da ingantaccen ilimi domin cigaban jihar.
Dukkanin ɗalibai da ke karatu a kwalejiji da jami’o’i mallakin jihar Kano kuma su ka kasance yan asalin jihar za su amfana da ragin kudin.
Bai wa ɓangaren ilimi muhimmanci na dga manufofin Injiniya Abba Kabir Yusuf wanda ya sha alwashin haka tun lokacin yakin neman zaben sa.
Labaran jiha
Jami’an Sojin Najeriya Sun Lalata Maboyar ‘Yan Bindiga A Katsina Da Sokoto


Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar lalata maɓoyar ƴan bindiga tare da wasu da dama a jihohin Katsina da Sokoto.

Jami’an sunƙato makamai da dama daga wajen yan bindiga.
Rundunar Operation Hadarin Daji sun samu narar ne a ranar 3 ga watan Agusta da mu ke ciki yayin da su ka kai hari ƙaramar hukumar Isa a jihar Sokoto.

Haka kuma runduna ta Takwas sun shiga Sabon Birni sannan su ka kusta dazukan Kusabunni, Tafkin Gawo, Alumdawa, Unguwar Mailete da Malamawa a nan ma su ka kora ƴan bindgan da ke wajen.

A jihar Katsina kuwa an samu nasarar kai hari garin Kore da ke ƙaramar hukumar Ɓatagarawa a nan ma su ka kuɓutar da wasu da aka yi garkuwa da su.

Mutane huɗu jami’an su ka yi nasarar kuɓutarwa waɗanda aka yi garkuywa da su a Unguwan Magudu da ke ƙaramar hukumar Ɗandume a jihar Katsina.
Jami’an sun samu nasarar ƙato makamai daga wajen ƴan bindigan tare da hallaka wasu yayin da aka kuɓutar da dabbobi da ake zargi masu garkwuan sun sace.
Labaran jiha
Yara 10 Sun Rasa Rayukan Su Sakamakon Cutar Da Ta Bulla A Kaduna


Kimanin yara 10 ne ‘yan tsakanin shekaru 3 zuwa 13 aka rahoto sun rasa rayukansu sakamakon bullar wata cuta mai shake numfashi a garin Kafanchan da ke karamar hukumar Jema’a ta jihar Kaduna.

Babban Daraktan lafiya (CMD) na asibitin ‘Sir Patrick Ibrahim Yakowa’, Dakta Isaac Nathaniel ne ya tabbatar da bullar cutar a Kafanchan inda ya ce har yanzun ba a gano musabbabin cutar ba.


Shugaban Karamar Hukumar Jema’a ta Jihar Kaduna, Honarabul Yunana Markus Barde, ya yi kira ga mazauna garin da su tashi tsaye sukai rahoton duk wani yaro mai shekaru kasa da 13 da ke fama da matsalar shakewar numfashi, ciwon makogwaro ko kuma yoyon majina a hanci ga hukumomin kiwon lafiya mafi kusa.

Shugaban ya bukaci mazauna garin da su lura da irin wadannan alamomin domin dakile yaduwar cutar da wuri kafin ta yi kamari.
Haka kuma an shawarci ma’aikatan kiwon lafiya a matakin farko a fadin kananan hukumomi, cibiyoyin maganin gargajiya, malaman addini, da iyaye da su dauki matakin da ya dace, ganin cewa, wasu iyaye da ‘yan uwa suna boye wasu daga cikin masu fama da cutar.
-
Mu shaƙata8 months ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Al'ada4 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labaran ƙetare4 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Labarai4 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini3 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Bidiyo3 years ago
Wanene Halilu Ahmad Getso? Ƴar cikin Gida
-
Labarai6 months ago
Akwai Jihohi Goma Da Zaɓen Gwamna Bai Kammala Ba A Najeriya Ko Har Da Kano?
-
Girke girke5 years ago
YADDA AKE LEMON SHINKAFA