Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya umarci hukumar zaɓe ta jihar Kkano da kada ta goyi bayan kowanne ɓangare.

Hakan ya fito daga bakin gwamnan yayin da ake rantsar da sabbin kwamishinonin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSEC.
Ya ce tun tuni majalisar dokokin jihar Kano ta tantance mutanen da aka rantsar,mutum guda ya rage a tantanceshi kafin a rantsar da shi.

An rantsar da su yau a ɗakin taro na Africa House da ke fadar gwamnatin Kano, yayin zaman majalisar zartarwa ta jihar Kano.

Ana sa ran gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi ne a shekarar 2021 mai kamawa.