Shugaban majalisar dokokin a Najeriya Ahmed Lawal ya bayyana cewar za a bi dukkanin matakan kariya don kaucewa kamuwa da cutar Korona a lokacin da ya rage kasa da awanni 24 da shugaban kasar zai gabatar da daftarin kasafin kudi na shekarar 2021.

Cikin tsarin da za a bi akwai kaucewa cunkoso wanda yace iya mutanen da suke da alaka da kasafin ne kadai za su halarci majalisar.

Ya kara da cewa za a gudanar da taron a kasa da awa guda, tare da bayar da tazara a tsakaninsu.

Ya cigaba za a takaita mutane  da za su yi rakiyar shugaban zuwa majalisar don kaucewa taruwar mutane a yayin gabatar da kasafin kudin.

A gobe Alhamis ne dai ake sa ran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gabatar da daftarin kasafin kudin shekarar 2021 mai kamawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: