Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa Yemi Osibajo zasu kashe naira bilyan 3 da milyan 200 a wajen tafiye tafiye.

Ofishin kasafin kudi na Najeriya ne ya fitar da kididdigar yadda shuwagabanni zasu kashe kudin wajen gudanar da tafiye tafiye na cikin gida dama kasashen waje
A ranar Alhamis ne shugaba Buhari ya gabatarwa da majalisun dokoki daftarin kasafin kudin da ake sa ran kashewa a shekara ta 2021.


