Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace likitoci biyu a jihar Kogi.
Ƙungiyar likitocin jihar ta tabbatar da sace Ebiloma Yahaya Aduku da aka sace a ranar Talata sai Kelechi Mgbahurike wanda aka sace a ranar larabar da ta gabata a cikin asibitin da suke aiki.
Ƙungiyar likiticin a jihar sun tabbatar da cewar ƴan bindigar sun nemi kuɗin fansa daga iyalan likitocin, kamar yadda suka bayyana a sanarwar da suka fitar.
sai dai kakakin yan sanda a jihar ya ce zai binciki lamarin kafin jin ta bakin rundunar.