Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Wata mata ta cefanar da jikanta miliyan ɗaya da ɗoriya

Wata mata ta sayar da jikanta akan naira miliyan daya da dubu dari   hudu kwanaki hudu da haihuwarsa a garin Cristian Duru  a jihar Imo.

Mahaifin yaron shi ya shigar da kara akan yana zargin matarsa Victoria da kashe masa ɗa bayan ta sanar da shi cewa dan ya mutu.

Sai dai kuma mahaifiyar yaron ta bayyanawa yan sanda cewa mahifiyar ta ce ta dauki d’an tare da sayar da shi akan naira milyan daya da dubu dari hudu.

Haka kuma tace kafin mahaifiyar tata ta dauki yaron saida tayi mata barazanar hallakata idan har ta tona mata asiri.

Tuni rundunar yan sanda a jihar fatakwakal ta samu nasarar ceto yaron cikin koshin lafiya tare da tsare matar da ake zargi  akan lamarin.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: