Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Ƴan fashi sun hallaka wani Darakta a Bauchi

 

Wasu da ake zargin ƴan fashi  ne sun hallaka wani darakta da ke aiki a Jami ar Tafawa Ɓalewa a jihar Bauchi

Mutanen sun tare Injiniya Hassan Sabo Jama are  yayin da yake kan hanyarsa ta kowa gidansa da ke Tudun Salmanu a garin Buchi.

Wani da al amarin ya faru a gabansa ya shaida cewar mutumin yayi kwarwa domin a zo a taimakeshi amma babu wanda ya je wajen har sai da mutanen suka gudu da motarsa.

An yi gaggawar kaishi asibitin  koyarwa da ke Bauchi kuma a can ne aka tabbatar da rasuwarsa.

Mai Magana da yawun yan sandan jihar DSP Ahmed Muhammad Wakili ya tabbatar da faruwar lamarin, y ace an halllaka mamacin ne da wuƙa da misalin ƙarfe goma na daren jihar Lahadi.

Ya ƙara da cewa tuni kwamishinan ƴan sandna jihar ya bada umarni don bicike a kan lamarin.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: