Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Ɗaliban firamare da sakandire sun koma makaranta a Kano, kwaleji da jami a za su koma ranar 26

A yau litinin ɗaliban firamare da sakadire har ma da islamiyya suka koma makaranta bayan kwashe watanni bakwai suna zaman gida sakamakon ɓullar cutar Korona a Najeriya.

Kamar yadda muka baku labarin cewar gwamnatin jihar Kano ta amince ɗaliban su koma ɗaukar darasu a makarantunsu daga ranar 11 ga watan da muke ciki.

A yau ɗalibai a jihar Kano sun koma makarantunsu tare da bin dukkan dokokin da aka bayar na bada tazara, wanke hannu da amfani da safar baki da hanci.

Mujallar Matashiya ta  zagaya wasu daga cikin makarantu a jihar Kano tare da zantawa da wasu daga cikin ɗalibai.

A wani labarin kuma gwamnatin jihar Kano ta bayyana buɗe manyan makarantun gaba da sakandire daga ranar 26 ga watan da muke ciki.

Jihar Kano ta shiga sahun jerin jihohin da ɗaliban makarantar firamare da sakandire suka koma karatu bayan tsawon lokaci da makaratun suka kasance a kulle sakamakon cutar Korona.

Gwamnati ta duba yuwuwar komawa makarantun ne bisa samun sauƙin masu kamuwa da cutar a Korona faɗin Najeriya.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: