Mawaƙi Abdul D One ya bayyana cewar ya kwashe shekaru goma sha uku yana waƙa, tun lokacin da ya samu asalin sunan D One a makarantar sakadire.

Yayin zantarwarmu da shi ya ce ya fara rubutun waƙa a shakarar 2007, sannan ya fara shiga ɗakin rera waƙa a shekarar 2009.

Ya rera waƙoƙi guda 100 da bakinsa.

Sai dai mawaƙin ya bayyana cewar ba zai iya tuna waƙar da ya fara rerawa  da bakinsa ba.

Cikin wata tattaunawar da mujallar Matashiya ta yi da shararren mawaƙin nan da ludayinsa ke kan dawo a masana antar fina finan Hausa wato Abdul D One ya ce waƙar Mahaifiya ya fi ƙauna a rayuwarsa.

Mawaƙin ya bayyana dalilinsa na cewar al’umma sun karɓi waƙar suna ƙaunarta kuma hakane ya sa yake matuƙar son waƙar saboda abinda mutane suke so shi yake ƙauna.

Zantawar tamu bata tsaya iya nan ba har sai da mawaƙin ya bayyana cewar ya yi waƙoƙi da sun haura guda ɗari 100 amma a cikinsu guda biyu rak ya fito a cikin faifan bidiyo.

A karo na biyu Abdul D One ya fito a waƙarsa ta Shalele, bayan waƙarsa ta farko da ya fito cikin faifan bidiyo wato Kece Tawa.

Waƙa ta gaba kuwa itace Zainabu Abu, wadda suka rerata tare da ubangidansa wato Umar M Shareef.

Ana sa ran za su fito tare a cikin faifan bidiyon waƙar wadda itace ta uku wanda D One ke fitowa a faifan bidiyo.

Domin masoyansa su kalla hakan ya sa mawaƙin ke wallafa waƙoƙinsa a shafinsa na youtube Abdul D One.

Leave a Reply

%d bloggers like this: