Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ne zai ci gaba da shugabantar majalisar Sarakunan Kano

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje yasanya hannu kan dokar da ta haramta tsarin karɓa-karɓa na shugabancin majalisar sarakuna a Kano.
Sabuwar dokar ta bawa mutane biyar damar naɗa sarki a kowacce masarauta saɓanin mutane huɗu da ke naɗa sarki a baya

Gidan shatima shi ne sakatariyar masarautar wanda a yanzu haka ake gyarawa.

Gwamnan Kano ganduje dai ya ƙirƙiri sabbin masarautu huɗu aka basu sanda a zamanin tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll.