Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labaran jiha

Gwamna Zulum ya ɗauki sabbin malaman makaranta a Borno

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya amince da ɗaukar sabbin malaman sakadire guda 776 a faɗin jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a Maiduguri bayan ganawarsa da jami an ma aikatar ilimi mai zurfi da hukumar kula da ilimin firamare a jihar.

Gwamna Zulum ya bayyana cewar za a tantance malaman kuma ba da jimawa ba za a bawa hukumar kula da ilimin firamare dama don ƙara ɗaukar sabbin malaman firamare a jihar.

Gwamnan y ace majalisar zartarwa a jihar ta amince da ƙara wa adin malaman makarantun gaba da sakadire zuwa shekaru 67 kuma tuni suka miƙa buƙatar hakan ga majalisar dokokin jihar.

 

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: