Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labaran jiha

Ruwan sama yayi awon gaba da gidaje da gonaki sama da 700

Aƙalla gidaje sama da 700 ne suka ruguje sanadin ambaliyar ruwan sama na bana a jihar Naija.

Unguwanni 57 lamarin ya shafa a ƙananan hukumomin Bosso da Paikoro.

Shugabar hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa reshen jihar Naija Lydia Wagami ce ta bayyana hakan yayin da take raba kayan tallafi ga waɗanda lamarin ya shafa.

Ta ƙara da cewa cikin wuraren da ruwan ya yiwa ta adi akwai gonaki wanda ruwan ya shafe kayan amfani masu tarin yawa.

Sannan ta roki mutanen da kada su sayar da kayan tallafin da aka basu ya kamata su yi amfani da shi ta hanyar da ya dace.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: