Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Zanga Zanga don kawo ƙarshen zub da jini a Arewa – An samu cikas a jihohi da dama

Gamayyar ƙungiyoyin Arewa da suka sirya tsunduma zanga zanga a yau domin kawo ƙarshen zub da jini a jiohin Arewa ta samu cikas.

A jihar Kano yan daba sun tarwatsa masu zanga zanga a unguwar Kabuga, bayan da mutane suka fara tattaki kuma ƴan daba ɗauke da makamai suka tarwatsasu.

Mutanen sun fito zanga zangar a yau wanda jihohi 19 na Arewacin ƙasar nan suka shirya yi.

Daga jihar Katsina kuwa ba a fita zanga zangar ba sakamakon taron siyasa da za a yi a yau, lamarin da ya sa ƙungiyoyin a can suka janye domin kaucewa afkuwar rikici a jihar.

Haka lamarin yake a jihar Yobe ba ba a fita zanga zangar ba, saboda jami an ƴan sanda ba su bada dama ba duba ga cewar akwai matsalar tsaro da ake fama da ita a jiar.

A jiar Kaduna kuwa an yi zanga zangar wanda mutane da dama suka fito ɗauke da kwalaye wanda ke nuni da cewar a kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabi Arewacin ƙasar nan.

Daga jihar Zamfara kuma mutane sun fito zanga zangar sai dai  ba su kai ga kammala tattakin ba kowa ya watse saboda mutuwar wani babban mai riƙe da madafun iko a jiar, hakan ya sa aka dakatar da zanga zangar a yau kuma ba a saka ranar da za a cigaba ba.

A jihar Adamawa kuwa mutanen ba su samu saƙon fita zanga zangar ba da wuri hakan ya sa suka mayar da tsarin zuwa gobe juma a bayan ganawarsu da kwamisinan ƴan sandan jihar.

A babban Birnin tarayya Abuja kuwa ministan Abuja je ya sanar da aramta zanga zangar don kaucewa yaɗuwar cutar Korona.

An shirya zanga zangar lumana a jihohin Arewa bayan matasa a kudancin ƙasar sun gudanar da zanga zangar kifar da sashen ƴan sanda na SARS kuma suka samu nasara

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: