Gwamnatin jihar Bayelsa ta bada umarnin rufe makarantun firamare da sakadire a faɗin jihar.
Hakan ya biyo bayan ambaliyar ruwan sama da ta mamaye makarantu a faɗin jihar.
Gwamnan jihar Douye Diri ya bada umarnin hakan bayan ya halarci wasu unguwanni a ƙaramar hukumar Yenagoa.
Gwamnan ya nuna damuwa matuƙa a bisa halin da ya tsinci al ummar a yankunan, kuma ya ce zai cigaba da kai ziyara dukkanin wuraren da abin ya shafa don nuna musu cewar gwamnatin na tare da jama ar jihar.
Sannan ya miƙa koken hakan ga fadar shugaban ƙasa don ganin an kawo masu ɗauki a bisa halin da suke ciki.
An buɗe makarantu a jihar a watan Oktoban da muke ciki bayan dawowa daga hutun dole na annobar Korona.