Labarai
Matsalar tsaro – A gobe za a tashi da Azumi


Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya umarci al ummar jihar da u tashi da Azumi a gobe Litinin.

Wannan ne karo na biyu da gwamnan ya bada umarnin bayan ganawarsa da shugabannin addinin musulunci da kirista.
Gwamnan ya buƙaci al ummar da su yi azumin ne don samun zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziƙi.

A baya bayannan ne dai gwamnan ya buƙaci shugaban ƙasa Buhari da ya sauya fasalin tsarin tsaron ƙasar don kawo ƙarshen matsalar tsaro a Najeriya


Labarai
Dola Ne Jami’an Tsaro Su Kara Kaimi A Kan Aikin Su-Tinubu


Dole Ne Jami’an Tsaro Su Ƙara Ƙaimi A Kan Aikinsu – Tinubu

Shugaban kasar Najeriya Ahmed Bola Tinubu ya ja hankali ga manyan jami’an tsaro ƙasar da su kara himma da dagewa don Samun tabbataccen zaman lafiya a kasar.


Shugaban ya sanar da hakanne yayin ganawarsa da shugabanin hukomomin tsaron kasar karo na farko a fadarsa da ke Abuja.

Yayin ganawarsa da manaima labarai bayan kammala zaman mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro yace shugaban sam ba zai lamunci yanayin da kasar take ciki ba.
Bola Tinubu ya ce bai dace kasar ta kara zama koma baya ba lokacin da sauran kasashen duniya ke ci gaba.
Ya kara da cewa wajibi ne a samu hadin kai tsakanin dukkanin sauran bangarorin tsaro ta fuskar tsaro.
Labarai
CBN Ya Musanta Batun Karya Darajar Naira



Babban bankin Najeriya (CBN) Ya musanta wata sanar wa da ta fita kan cewa darajar Naira ta karye a hukumance.


Hakan ya fito ne ta bakin Mukaddashin Daraktan bankin Abdulmuminu,

Abdulmuminu, yace ko a jiya Laraba an siyar da dala ɗaya a kan naira 465.
Ya kuma kara da cewa Rahoton da ya fita kan sanarwar karyewar darajar Naira ba gaskiya ba ne.
Bankin ya shawarci Mutane da su yi watsi da Rahoton da su ka ji kan karyewar darajar Nairar.
Labarai
Mutane 7 Sun Rasu A Wani Hatsari Da Auku A Bauchi-FRSC


Hukumar kiyaye hadurraya kasa FRSC ta ba bayyana cewa mutane takwas ne suka rasu bayan da wani hatsari ya auku a jihar Bauchi.

Kamar yadda hukumar ta kiyaye hadurra ta bayyana ta ce hatsarin ya faru ne akan babbar hanyar Darazo zuwa Bauchi ajiya Laraba 31 ga watan mayu.


Ta ce hatsarin ya faru da misalin karfe 1:43 na rana inda bayan haduwar motar kirar Hilux da kuma wata motar daukar fasinja Golf.

Sannan hatsarin ya rutsa da mutane 14 mata bakwai maza bakwai inda maza hudu suka rasu da mata hudu ciki harda yara kanana.
Sannan akwai wadanda suka Samu raunuka a jiki.
Sai dai kamar yadda hukumar ta kiyaye hadurra ta bayyana ta ce ta mika sauran masu rauni izuwa asibitin Darazo.
A ko da yaushe hukumar kiyaye hadurran ta na bayyana cewa direbobi su guji gudun wuce kima duba da yanayin damina ne a yanzu.
-
Al'ada4 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labaran ƙetare4 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Mu shaƙata4 months ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labarai4 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Bidiyo3 years ago
Wanene Halilu Ahmad Getso? Ƴar cikin Gida
-
Addini3 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Labarai2 months ago
Akwai Jihohi Goma Da Zaɓen Gwamna Bai Kammala Ba A Najeriya Ko Har Da Kano?
-
Labarai1 year ago
Da Ɗumi-Ɗumi A Na zargin Bam Ya Tashi a Unguwar Sabon Gari A Kano Yanzu