Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da cewar tana yin duk mai yuwuwa don ganin an samu zaman lafiya mai dortewa a jihar.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyyana hakan a yayin zaman majalisar zartarwa da ya gudana yau a ɗakin taro na Afrika House.
Ganduje ya ce sun zauna da shugabannin ɓangare daban daban a jihar Kano tare da nuna musu muhimmancin zaman lafiya kuma za su yi aiki da jami an tsaro don ganin an tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar.

Ya ce jihar Kano gari ne na zaman lafiya, kuma ya buƙaci kowa da kowa ya zauna lafiya domin babu wani abu da ya fi zaman lafiya.

Daga ƙarshe gwamna Ganduje ya kafa kwamitin zaman lafiya, wanda ya haɗar da masu madafun iko a ciki.