Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewar tana nan daram wajen ganin ta sanya idanu don tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar

Kwamishinan ƴan sandan jihar Habu A. Sani ne ya bayyana hakan a wata zantawa da yayi da ƴan jaridu dangane da hargitsin da ya faru na masu zanga zangar #ENDSARS a Kano.

Kwamishinan yace sun kama wani likita da yayi harbi da bindiga a yayin zanga zangar.

Sai dai ya musanta labaran da ake yaɗawa cewar an kashe mutane huɗu a yayin zanga zangar wanda yace basu samu rahoton hakan ba.

Ya ce sun samu mutane 6 wadanda suka samu rauni ciki har da baturen yan sanda wanda yayi kokarin kubutar da wasu mata da yara a wani gida.

Tun safiyar jiya talata ne dai aka kunnawa tayoyi wuta a wasu daga cikin titunan jihar Kano, Mujallar Matashiya ta gano wasu motoci da aka ƙona tare da farfasa gilasan motoci.

A wani labarin kuma rundunar yan sandan jihar Kano ta bayyana cewar bas u da hannu wajen kisan wani matashi da ke unguwar ƙofar mata a kano.

Idan baku manta ba a ranar Litinin mun baku labarin cewar, al ummar unguwar ƙofar mata da ke kwaryar birnin Kano sun yi zargin ƴan sanda da hallaka wani matashi a unguwar, lamarin da ya sa suka tashi da zanga zanga tare da ƙona tayoyi a kan titi.

Sai dai mai kakain ƴan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya musanta wannan zargi tare da cewar jami ansu sun je samame don kama yan saba  bayan sun samu labarin ana fadan daba, lamarin da ya sa ƴan daban suka yi sanadiyyar rasuwar mamacin.

Ya kara da cewa bayan jami ansu sun ziyarci wajen sun samu an sokawa matashin wuƙa a ciki, da wasu sassa na jikinsa, sai wani jami I da aka yanka da wuƙa wanda tuni aka kaishi asibiti.

Sannan sun samu nasarar kama mutum biyu daga cikin yan daban wanɗanda aka samesu da wuƙa a jikinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: