Gwamnatin jihar legas ta sanar da cewar mutane 25 ne suka samu rauni a yayin zanga zangar da aka gudanar jiya a garin.

Gwamnan jihar Babajide Sanwo Olu ne ya bayyana hakan a yau bayan ya ziyarci waɗanda suka samu raunin a yayin zanga zangar.

Gwamnan ya musanta labarin mutuwar mutane da aka ce an harbe a yayin zanga zangar, bayan gwamnatin jihar ta sanar da dokar hana zirga zirga ta awanni 24.

An zargi sojoji da harbin mutane a Lekki wanda rundunar sojin ta musanta zargin.

Ko da a safiyar yau ɗinnan wasu da ake zargin yan daba ne sun ƙona gidan talabiji na TVC, da ma aikatar jiragen ruwa har ma da ofishin hukumar kwastam.

Leave a Reply

%d bloggers like this: