Wasu matasa a jihar Kaduna sun gudanar da zanga zangar kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar.

Lamarin ya faru a yau, bayan gamayyar ƙunyoyin Arewa sun dakatar da gudanar da zanga zangarsu a jihohin arewacin ƙasar.

Matasan sun yi tattaki a tsakiyar birnin jihar Kaduna sannan suka nufi sakatariyar ƴan jaridu tare da bayyana dalilin da yasa suka shiga zanga zangar.

Matasan sun buƙaci shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari yay i cikakken bayani a kan matakin da aka dauka don kawo ƙarshen matsalar tsaro a arewacin ƙasar.

Zanga zanga a Najeriya ta yi ƙamari a ƴan kwanakinnan tun lokacin da wasu jihohin kudancin ƙasar suka nemi a soki jami an ƴan sandan sashen SARS wanda tuni aka rushesu tare da kafa dakarun SWAT da a yanzu haka suka fara karɓar horo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: