Aƙalla mutane 200 mujallar Matashiya ta yaye bayan ta kammala basu horo kyauta a kan sana o in dogaro da kai.

Matasa maza da mata ne suka amfana da sana o in da aka horas a Mujallar Matashiya daga shekarar 2019 zuwa 2020.

Cikin sana o in da aka horas da matasan akwai masu ɗaukar hoto mara motsi da hoto mai motsi sai masu haɗa man shafawa da maganin kyazbi,

Sauran sana o in sune sana ar kwalliya da sarƙa da ɗan kunne sai kuma waɗanda aka bawa horo a kan aikin jarida.
Shugaban mujallar Matashiya Abubakar Murtala Ibrahim ya bayyana cewar burinsa a kullum bai wuce samawa matasa aikin yi ba.
Ya ƙara da cewa a kowanne lokaci babu abinda yake sakashi farin ciki illa ya ga matasa sun dogara da kansu a don haka ya sadaukar da lokacinsa da tunaninsa da abinda ya mallaka don ganin matasan sn tsaya da ƙafarsu.
Wannan dai karo na uku kenan da mujallar Matashiya ke yaye matasa, ko da a baya ma sai da mujallar ta yaye matasa 300 waɗanda aka horas a fanni daban daban.
Wasu daga cikin ɗaliban da suka samu horon sun bayyana farin cikinsu a kan lamarin.
Babangida Aminu guda ne cikin mutanen da aka bawa horo a kan ɗaukar hoto mai motsi kuma ya bayyana cewar zai zage damtse wajen ganin ya cigaba da gudanar da aikinsa, kamar yadda a yanzu haka ya buɗe kamfani mai zaman kansa wanda suke sana ar ɗaukar hoto.
A yayin taron an karrama wasu muhimman mutane da suka bawa mujallar gudunmawa.